Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ITALIYA: An Ceci Bakin Hauren Da Suka Kage a Teku


Tsirar Wasu Bakin Haure

Kasar Italiya da Fransa sun yi ayyukan ceton bakin haure fiye da 1,400 da suka kage a kan tekun Mediterranean dake daura da tekun Libya bayan kwale-kwalensu ya sami matsala.

Jami’an Italiya sun ce Sojojin ruwa da dogarawan Teku sun ceto mutane 1,200 ta hanyar amfani da kwarewa suka kuma mika su tashoshin jiragen ruwan kasar Italiyar.

A wani gefen kuma jirgin ruwan Faransa ya cafko wani jirgin ruwa mai dauke da bakin hauren sama da mutum 200 da wasu mutane biyu da ake zargin sune masu safarar mutane, suka kuma mika su ga hukumomin Italiya.

Fiye da bakin haure 150,000 ne suka shiga Italiya a bara, sun ce a ‘yan tsakanin nan mutane 5,000 ne suke samun isa kasar duk mako har nan da watanni 4, wanda yawan su zai kai 200,000 nan da karshen shekarar nan.

Tun bayan janye kudin tallafin ceton bakin hauren Tarayyar Turai a shekarar 2014, kasar italiya ce ke fama da bubbugar bakin haure akan tekunta saboda kusancinta da arewacin Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG