Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Chafke Mutanen Da Suka Kashe Jakuna Fiye Da Dubu Daya Don Safarar Su Zuwa China


‘Yan Sandan Najeriya
‘Yan Sandan Najeriya

Hukumar hana fasa kwabri ta damke wasu mutane biyu a jihar Kebbi da suke tuhuma da yanka Jakuna kimanin dubu daya da aka kiyasta kudin su fiye da naira miliyan 42 suka yi safarar naman su.

KEBBI, NIGERIA - A jihar kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya ne jami'an hukumar hana fasa kwabri ta kama wasu mutane da suka kashe Jakuna da kuma safarar naman su abinda kwantorolan hukumar Joseph Attah ya ce ya sabawa doka.

Wannan na zuwa ne lokacin da masana ke ganin cewa yawan take dokoki da ake yi baya rasa nasaba da abinda ya jefa kasar cikin kalubale ta fuskoki daban daban abinda ke kara jefa ‘yan kasa cikin kuncin rayuwa.

A halin da ake ciki yanzu rayukan ‘yan Najeriya musamman talakawa na ci gaba da fuskantar halin kunci sanadiyar matsaloli da suka yi wa kasar kaka-gida kama daga matsalar rashin tsaro, tsadar abinci, tsadar man fetur, rashin wadatattar wutar lantarki da dai makamantan su.

Wannan kuma bai hana ‘yan kasar rufe idanu suna aikata wasu ayukka da dokokin kasa suka hana ba, ba tare da la'akari da illolin da yin hakan kan iya haifarwa ba.

Masu Safarar Jakuna A Najeriya
Masu Safarar Jakuna A Najeriya

Aminu Salihu direban motar tirela da ta dauko naman jakunan ya ce baya da masaniya akan ko menene ya dauko. Shi kuwa wanda ke rike da naman Sylvester ya ce sako ne kawai aka bashi ya isar.

Jama'a dai na ganin da ‘yan Najeriya shugabanni da wadanda ake shugabanta zasu mutumta dokokin kasa da al'amurra za su gudana yadda ake muradi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

An Chafke Mutanen Da Suka Kashe Jakuna FIye Da Dubu Daya Don Yin Safarar Su Zuwa China
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG