Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An ci gaba da tattaunawa a tsakanin mashawarta na Sudan da Sudan ta Kudu


Shugaban tawagar Sudan ta Kudu, Pagan Amum, a hagu, tare da shugaba Omar al-Bashir a Khartoum, Sudan, ranar alhamis 22 Maris, 2012, lokacin wata ziyarar da 'yan Sudan ta Kudu suka kai domin shirya ganawa a tsakanin shugabannin kasashensu biyu.

An ci gaba da tattaunawar duk da rahotannin da aka samu na sabon fada da kuma tababa kan janyewar Sudan baki daya daga yankin Abyei da ake rikici a kai.

An ci gaba da tattaunawa a tsakanin mashawarta na Sudan da Sudan ta Kudu jiya laraba karkashin kulawar masu shiga tsakani na Kungiyar Tarayyar Afirka, duk da rahotannin da aka samu na sabon fada da kuma tababa kan janyewar Sudan baki daya daga yankin Abyei da ake rikici a kai.

An fara tattaunawar kusan awa uku a makare jiya laraba yayin da ake tankiya. Babban jami’in shawarwari na Sudan ta Kudu, Pagan Amum, yace an takaita tattaunawar farko ga batutuwan da suka shafi tsarin yadda za a yi shawarwari.

Tattaunawar da aka yi a can baya ta wargaje a watan da ya shige a bayan kazamin fadan da sassan biyu suka gwabza a bakin iyakarsu, har suka yi kusan komawa ga yaki gadan-gadan. Fadan shi ne mafi muni da aka gani tun lokacin da Sudan ta Kudu ta balle daga Sudan a watan Yuli.

Fargabar komawa ga yaki ta sa Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kudurin da ya umurci sassan biyu da su tsagaita wuta su koma kan teburin shawarwari.

Babban jami’in shawarwari na Sudan ta Kudu ya nemi da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa ma Sudan takunkumi saboda ta keta kudurin Kwamitin Sulhun. Amma yace a shirye yake ya ci gaba da shawarwarin da ya bayyana a zaman yana tafiya sosai.

Wakilan Sudan ba su ce uffan ba, amma sun bayarda rubutacciyar sanarwar dake jaddada kudurin Sudan na warware dukkan batutuwan da sassan ke sabani a kai ta hanyar tattaunawa, tare da yin alkawarin rungumar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG