Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Gaba Da Zanga-zanga a Rasha Kan Tsare Sergei Furgal


Dubban masu zanga-zanga sun sake fitowa zanga-zanga a birnin Khabarovsk da ke gabashin Rasha ranar Asabar 1 ga watan Agusta tsawon karshen makonni 4 kenan a jere don nuna rashin amincewarsu da yadda Shugaba Vladimir Putin ke tafiyar da harkokin siyasar kasar.

Mazauna birnin Khabarovsk, mai tazarar kilomita kimanin 6,110 gabas da birnin Moscow, ba su ji dadin yadda aka kama tare da tsare gwamnan yankin Sergei Furgal ba a ranar 9 ga watan Yuli bisa zargin kisan kai, laifin da ya musanta.

Kamen gwamnan, da magoya bayansa suka ce siyasa ce, ya janyo zanga-zanga a kan tituna tsawon makonni, abinda ya zama kalubale ga gwamnatin Kremlin da ke kokarin magance matsalar tattalin arziki a kasar sakamakon barkewar annobar cutar coronavirus.

Hukumomin birnin sun kiyasta cewa kusan mutum 3,500 suka yi zanga-zangar. Wasu kafafen yada labaran kasar sun ce yawan mutanen ya wuce 10,000, amma sun ce yawan ya ragu idan aka kwatanta da makonnin da suka kagaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG