Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci ISIS Da Yaki


Wani sashi a fafatawa ta karshe a yaki da ISIS

Abin kamar almara; yanzu kungiyar ISIS, wadda a baya ta girgiza duniya, har ta kafa babbar daularta, wadda ta kunshi akasarin kasar Iraki da sassan Siriya, ta zama tarihi, a kalla ta fuskar daula da dakaru.

Dakarun SDF da ke yaki da ISIS a Siriya tare da taimakon Amurka, sun yin shelar yin galaba kan kungiyar ‘yan ta’addan ISIS a zahirance, bayan an shafe tsawon dare ana ta luguden wuta na karshe, to amma dakarun na SDF sun kuma yi gargadin cewa wani fadan na nan tafe.

A jerin dare na karshen, an yi ta ruwan bama-bamai kan dan dan abin da yankin kasar da ISIS ta ayyana a matsayin daularta, ta yadda sai haske ake gani a sararin saman garin Baghuz da ke arewa maso gabashin Siriya.

Hasali ma, tun daga safiyar jiya Asabar, babu abin da aka fi gani a filin Allah kamar tarkacen ababen hawa da su ka kone, da tantunan kwana da kuma sauran kaddarorin iyalan ‘yan ta’addan na ISIS.

Dakarun na SDF sun kafa tutarsu a kan daya daga cikin gine-gine kalilan da har yanzu ke tsaye, inda su ke ta cigaba da bukin kawo karshen kungiyar ta ISIS.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG