Accessibility links

An Ci Zarafin 'Yan Jarida a Sokoto


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya na magana da 'yan jarida

A wani abun da ba'a saba gani ba an kulle wasu 'yan jarida a fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi yayin da shugaban kasa ya kai ziyara.

Yayin da shugaban kasar Najeriya ya kai ziyara fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammed Sa'ad Abubakar III wani lamarin da ba'a saba gani ba ya faru.

Ilahirin duk 'yan jarida da suka je fadar domin ziyarar shugaban kasa an kullesu a wani daki kuma babu wani dalili da aka bayar na yin hakan.

Amma daga baya an bar 'yan jarida biyar su fito daga dakin da aka tsaresu wadanda suka hada da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Sanyiina inda ya samu daukan sautin jawaban da suka rage.

Shugaban 'yan jarida a jihar Sokoto Bello Muhammed yace wannan shugaban kasa ne da aka ce shi ne na farko da ya sanya hannu ga dokar da ta ba 'yan Najeriya 'yancin fadan albarkacin bakinsu da na jarida. To amma abun da ya faru da wasu halayen gwamnatin sun nuna vewa shugaban ya sanya hannu ne kawai bashi da nufin barin dokar ta yi aiki. Idan har aka ce dan jarida ba zai shiga inda ake aiki ba ko zantawa to yaya zai san abun dake faruwa balantana ya sanarda mutane. Shugaban tun karfe daya suke jiransa amma bai iso Sokoto ba sai karfe biyar kuma duk da makarar da yayi an sake kulle 'yan jarida.

Watakila abun ganewa shi ne 'yan Najeriya ba'a son su san abun dake faruwa a gwamnatance. Abun da suka yi abu ne da yakamata kowa yayi tur dashi. Bello Muhammed yace an wulakanta 'yan jarida domin bayan ma shugaban kasa ya kama ganawa da sarkin Musulmi sai da aka roki Dr Ruben Abati kafin a sako sauran 'yan jaridan.

XS
SM
MD
LG