Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cigaba Da Zanga-Zanga Kan Kisan Bakaken Fata A Amurka A Dare Na Hudu


Zanga-zanga kan kisan bakaken fata a Amurka
Zanga-zanga kan kisan bakaken fata a Amurka

Duk da ruwan sama mai tafe da sanyin watan Disamba, an cigaba da gudanar da zanga-zanga a biranen Amurka a dare na hudu a jere don nuna bacin rai kan kisan bakaken fata da ake zargin 'yan sanda fararen fata da aikatawa

Masu zanga-zanga da dama sun sake fitowa da daren jiya Asabar a wasu biranen Amurka ciki har da New York, da Washington, a daidai lokacin da ake tunawa da wani bakar fatar kuma da dan sanda farar fata ya kashe.

Abokai da dangin Akai Gurley dan shekaru 28 da haihuwa sun yi masa bankwana, a wurin jana'izarsa a Brooklyn na birnin New York.

Jami'in 'yan sandan Rookie da ke birnin na New York mai suna Peter Laing, ya bindige Gurley har lahira, a matakalar wani bene na rukunin gidajen haya da ake kan ginawa a watan jiya.

Jami'an 'yan sanda sun ce ba a zargin Gurley da aikata wani laifi, ya mutu ne lokacin da bindigar dan sandan ta tashi cikin tsautsayi.

To amma wata jaridar birnin New York ta ce dan sanda Laing ya dan bata lokaci kafin ya kira motar daukar majinyaci.

Babban Alkalin Brooklyn ya ce masu bin ba'asin shari'a ka iya tuhumar dan sanda Laing da laifuka.

Masu zanga-zanga a birnin na New York dai sun jaure da ruwan sama na watan Disamba mai sanyi a jiya Asabar don yin zanga-zanga kan mutuwar ta Gurley da kuma hukuncin da wasu rukunonin masu bin ba'asin shari'a su ka yanke na wanke wasu 'yan sanda farar fata da su ka kashe wasu bakaken fatar kuma biyu. A birnin Washington masu zanga-zanga sun katse wata mahadar hanya na wani dan lokaci yayin da su ke maci a birnin.

XS
SM
MD
LG