Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An cika shekara daya kisan gillan da Breivik ya yi a kasar Norway


Anders Behring Breivik
Anders Behring Breivik

Yau lahadi kasar Norway ta cika shekara daya da harin bom da kuma kisan gilla da aka yi, da ya yi sanadin rasuwar mutane 77

Yau lahadi kasar Norway ta cika shekara daya da harin bom da kuma kisan gilla da aka yi, da ya yi sanadin rasuwar mutane 77, inda Firai Ministan kasar Jens Stoltenberg yace kasar ta tunkari wannan bala’in ta wajen jadada burinta na damokaradiya da kuma hakuri da juna.

Yayin ajiye furanni a makabartar, Mr. Stoltenberg yace an kai hare haren ne da nufin sauya kasar Norway, amma burin wanda ya kai harin bai cika ba, kasancewa al’ummar kasar Norway sun maida martani da wajen kare abinda suke darajantawa.

Ranar 22 ga watan Yuli shekara ta dubu biyu da goma sha daya Anders Behring Brelvik ya tarwatsa bom kusa da wani ginin gwamnati a Oslo ya kashe mutane takwas. Daga nan ya budewa wadansu mutane wuta ya kashe 69 akasarinsu matasa a wani sansanin matasa dake tsibirin Utoeya.

Breivik wanda shekarunsa 32 a lokacin kai harin, ya amsa aikata kisan gillan, da cewa, daidai ne sabili da wadanda ya kashe suna kokarin maida Norway kasar Musulmi.

XS
SM
MD
LG