Accessibility links

An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta da Kungiyar Boko Haram


Wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka capke

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar Ahalis Sunna da aka fi sani da Boko Haram

Rahoton da muka samu ya ce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar Ahalis Sunna wadda aka fi sani da suna Boko Haram.

Wannan matsayin da aka cimma ya biyo bayan shawarwarin da suka wakana tsakanin kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa musamman domin neman sulhu da kungiyar a karkashi shugabancin Alhaji Kabiru Tanimu Turaki da kuma wakilin kungiyar Imam Mohammed Marwana.

Bayan shawarwarin wakilin kungiyar Imam Marwana ya tabbatar da cimma yarjejeniyar a cikin firar da suka yi da wakilin Muryar Amurka.Ya tabbatar wa al'umma cewa takaddama dake tsakaninsu da gwamnatin tarayya ta zo karshe da ikon Allah.Ya ce daga lokacin da yake magana an tsagaita wuta kuma ya karbi kayan fada da abubuwan dake fashewa daga mujahidansu domin tabbatarwa gwamnati cewa sun daina fada kuma za'a samu salama. Imam Marwana ya nemi gafara daga wadanda suka rasa 'yan'uwansu sanadiyar tashin tashinar. A nasu bangaren ya ce suma sun yafe abubuwan da aka yi masu.

Sai dai wakilinmu ya janyo hankalin Imam Marwana kan rahoton da ya fito daga jihar Yobe cewa an kashe 'yan makaranta 29 da malaminsu kuma ana zargin 'yan kungiyarshi da aikata wannan ta'asa amma ya musanta rahoton. Ya ce basu da hannu game da kashin da aka yi a Yobe. Ya ce su basu da masaniya game da lamarin. Da aka nemi ya ba da tabbaci cewa wasu 'yan kungiyar ba zasu buturewa yarjejeniyar da aka cimma ba sai ya ce komene 'yan kungiyar zasu yi sai su shugabannin sun sani sun kuma amince. A cewarsa 'yan kungiyar ba su ne ke iko da kansu ba. Ya ce bashi da tunanin cewa wani mujahidi zai buture wa tafiyar da suka dauko yanzu.

Shi ma shugaban kwamitin neman sulhu da kungiyar da gwamnatin tarayya ta kafa Alhaji Kabiru Tanimu Turaki ya btabbatar da cimma yarjejeniyar. Ya kuma ce gwamnati zata yi iyakacin kokarinta domin dakarunta su kiyaye da yarjejeniyar.

To amma can baya an sha jin labarin cimma yarjejeniya da kungiyar sai shugabansu Shaikh Abubakar Shekau ya fito fili ya ce ba dasu aka yi ba kuma shi bai san Imam Mohammed Marwana ba. Yanzu dai sai asa ido a ga yadda wannan sabuwar yarjejeniya zata tabbata.

Ga karin bayani daga Umar Faruk Musa.

XS
SM
MD
LG