Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cire Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya


Nigeria Elections

An Kori Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Sulaiman Abba, daga munkamisa, na shugaban 'yan sandan Najeriya.

Kakakin shugaba GoodLuck Ebele Jonathan, Dr. Reuben Abati, ne ya fitar da sanarwar cewa shugaba Goodluck Jonathan, ya sauke Sulaiman Abba, nan take kuma an nada Mr. Solomon Arase, a matsayin mai riko har wani lokaci.

Daga dukkan alamu abun yazo da mamaki koda yake an danyi harsashen cewa irin hakan zai iya faruwa, bincike ya nuna cewa Sulaima Abba, bai san an cire shi saqi da ya gani a kafofin yadda labarai.

Sulaiman Abba, dai an nada shi a matsayin sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, ne kasa da shekara daya kuma ba'a fadi dalilin cire shi ba.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

XS
SM
MD
LG