A yayin wani taron jam’iyyar CNDP da aka yi da yammacin ranar Juma’a 3 ga watan Yuli ne shugaban hukumar zabe ta kasa ya bayyana wa wakilan jam’iyyun da suka halarci wannan zama cewa hukumar ta CENI ta dage zaben kananan hukumomin da ya kamata a gudanar a ranar 1 ga watan Nuwamba na shekarar 2020 zuwa ranar 17 ga watan Janairu na shekarar 2021.
Me Issaka Sounna, ya ce rashin isasshen lokacin shirya zaben kananan hukumomi kamar yadda ya dace ya sa hukumar zabe dage wannan rana zuwa gaba amma kuma za a gudanar da zaben ‘yan Majalisar Dokoki hade da zagayen farko na zaben Shugaban kasa a ranakun da aka bayyana a baya, wato 27 ga watan Disamba na shekarar 2020 kafin a je zagaye na biyu a ranar 21 ga watan Fabarairu na shekarar 2021 .
“Ya kai Firai Minista, jam’iyyun siyasa sun kai 150 a Nijer mai yiyuwa da kyar za a samu jam’iyyu 20 ko 50 daga cikinsu wadanda zasu shiga zaben Shugaban kasa da na ‘yan Majalisa. Sauran jam’iyyu kusan 120 ba a banza aka kafa su ba. Wadannan jam’iyyu da magoya bayansu sun kagu su ga an shirya zaben kananan hukumomi musamman a jihohi domin su samu wakilai a majalisun karkara. To so kuke ku hana mu samun kansiloli? Ba mu yarda ba da wannan tsarin ba.” Shugaban jam’iyyar PNA Al’umma ta kawancen jam’iyyu masu mulki, Sanoussi Tambari Jakou kenan a lokacin da ya ke maida martani akan sabon jaddawalin.
Shi ma shugaban gungun jam’iyyu ‘yan baruwanmu, Hambaly Dodo, ya bayyana rashin gasmuwa da sabon jaddawalin na hukumar zabe.
To sai dai jam’iyyar PNDS Tarayya a ta bakin sakatarenta mai kula da sha’anin zabe Boubakar Sabo, na ganin hujjojin da hukumar zabe ta dogara da su wajen dage zaben kananan hukumomi sun dace da yanayin da ake ciki a yau.
Ga cikakken rahoton cikin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 06, 2023
NIJAR: Yawan Matan Da Ke Mutuwa A Yayin Nakuda Ya Ragu.
Facebook Forum