Accessibility links

An Danganta Tsawon Lokacin Da Uwa Tayi Tana Ba Jaririnta Nono Da Girma Nagarin Yara


Uwa tana shayar da jariri

Wani bincike daga kasar Greece ya nuna cewa yaran da aka basu nono har tsawon fiye da wata shida sun nuna kaifin kwakwalwa, iya amfani da harshe, da kuma motsa jiki lokacin da suke kan girma fiye da wadanda basu sami wannan shayarwas ba.

Wani bincike daga kasar Greece ya nuna cewa yaran da aka basu nono har tsawon fiye da wata shida sun nuna kaifin kwakwalwa, iya amfani da harshe, da kuma motsa jiki lokacin da suke kan girma fiye da wadanda basu sami wannan shayarwas ba.

Wani bincike da ya gabata ya nuna cewa tunani mai kyau da kuma iya tuna abubuwa sai dai ba a fahimci yadda wannan ya shafi magana da tafiya ba.

Masu binciken sun bayyana cewa, wannan sabon binciken bai tabbatar da cewa bada nono ne ya kawo wannen kaifin hankalin ba, sai dai ya nuna cewa suna da dangantaka.

A fadar Dr. Dimitri Christakis, farfesa a sashen maganin yara na jami’ar Washington da kuma direkta na maaikatar lafiyar yara, halaye da girmasu a wurin bincike na seattle, yace, “A tunani na, shaidun da suke a hannu yanzu sun isa su sa mu rufe littattafan amfanin shayas da yara nonon uwa, mu mayas da hankulanmu wajen yadda zamu zuga iyaye su shayas da yaran su domin dukan rahotonnin binciken suna nuna irin ribar da yara ke samu a duk lokacin da suke shan nonon iyayensu.”

Dr. Dimitri Christakis, ya bayyanawa Reutas a takardar wayar iska cewa tabbatatce ne cewa, “Shan nono yana da taimako wajen kare lafiyar yara.”

Domin fitar da rahotonsu, Dr Leda Chatzi daga Jami'ar Crete da abokan aikinta sun yi amfani sakamakon wani dogon bincike da ya kunshi mata 540 da yaransu.

Yayinda jariran suke wata tara, masu binciken sun tambayi iyayen mata lokacin da suka fara bada nono. Da yaran suka kai wata 18, masu binciken sun tattara sauran bayyanan.

Masanan kwakwalwa suma sun gwada iyawa, yadda yaran ke amfani da harshensu da yadda suke amfani da gabobin jikunansu lokacin da yaran suka kai wata 18.

Kimanin kashi 89 daga cikin dari na jariri sun sha nono. Kashi 13 cikin 100 daga cikinsu sun sha nono na kasa da wata daya, kasha 52 daga cikin 100 na su sun sha nono na tsakanin wata daya da wata shida kana kuma kasha 35 daga cikin 100 sun sha nono na fiye da wata shida.

A cikin gwajin, yaran da aka basu nono sune suka fi samun maki ta wajen kaifin kwakwalwa, iya yin magana, da kuma iya amfani da gabobin jiki fiye da yaran da basu sha nono ba.

Yaran da suka sha nono na tsawon fiye da wata shida kuma sun nuna hazaka fiye da sauran, a fadar rahoton da masu binciken suka fitar a mujallar Epidemiology and Community Health.
XS
SM
MD
LG