Accessibility links

Tagwayen Bincike a Amurka Sun Gano Yadda Kwayar Cutar HIV Ke Zama Kanjamau


Wasu yara masu fama da cutar kanjamau

Masanan kimiyya na Amurka sun gano yadda HIV ke kauda shirin kariyar jiki na mutum wanda yake haifas da kanjamau.

Masanan kimiyya na Amurka sun gano yadda HIV ke kauda shirin kariyar jiki na mutum wanda yake haifas da kanjamau. Gano wannan zai iya kai ga bullowar sababbin hanyoyin warkarwa da kuma bincike na kanjamau, cutar da ta shafi mutane miliyan 35 a kewayen duniya.

A maimakon kashe kwayoyin garkuwar jiki da ake kira CD4 T cells, yawancin barnar da HIV ke yi na faruwa ne lokacin da kwayar cutar tayi kokari ta kashe garkuwar jikin kuma ta kasa, wannan yunkurin sai ya haifas da wani mayas da murtani da garkuwar jikin ke yi inda take hallaka kanta a yaki da ake kira pyroptosis.

Rohoton binciken da suka fito tare a mujallar kiymiya mai suna Scientifi Journals Science and Nature, yana nuna cewa za’a iya gwada karkata maganin da kamfanin magunguna na Vetex Pharmaceutical Inc wanda kuma aka rigaya aka gwada a kan mutane masu farfadiya zuwa maganin ciwon kanjamau.

“Kasidunmu mun kunshi ginshiikan abubuwan da ke kawo kanjamau wanda kuma shine rashin CD4 T Cells” in ji Dr Warber /green na Gladson Intitutes, wata ma’aikatar bincike ba don neman riba ba dake San Francisco inda kuma a wurin ne aka yi duka binciken biyu.

Dr. Anthony Fauci, direktan wata maaikata ta cututtuka, yace, takardar ta tanadi ‘babban’ amsa ga tambayar da masanan kimiyya ke nema tun da aka gano wannan kwayar cutar a shekara ta 1983.

Greene yace masana sun yi shekaru da yawa suna tunanin cewa kwayar cutar HIV na kashe garkuwar jiki ne ta wurin juya garkuwar jikin ta zama wurin kyankyashe kwayoyin HIV.

CD 4 T cells kadan ne suke mutuwa ta wannan hanyar. A cikin jerin binciken da aka yi a cikin saifa, da wadansu gabobin jikin mutanen da suka kamu da HIV, masana kimiyan Gladstone sun ganoyawancin binciken da akayi a kan marasa lafiya dauke da cutar HIV, masanan Gladson sun gano cewa ainihin wannan barna tana faruwa ne a cikin wadansu irin CD 4 T cells da ake kira “yan kallo”

Wadannan kwayoyin garkuwan jikin suna cikin hutunsu, saboda haka, yayinda kwayar HIV ta kawo hari, sai ta kasa cin nasara kansu ta koma.

Sai dai kuma barnar ta rigaya ta faru. Wadannan kwayoyin garkuwar jikin da aka kai wa hari sai su fitar da wani irin sinadari wanda ke yin amfani da wani sinadarin kua da ake kira caspase-1 wanda ke kawo kwayoyin garkuwar jikin su kashe kansu, wani abu da ake kira pyroptosis.

“Garkuwar jikin suna kashe kansu a cikin wani kokarin kare jikin,” in ji Greene. Ya kara da cewa “Wannan yunkurin da bai ci nasara ba yakan haifas da neman gudummuwa daga sababbin CD 4 wadanda kuma ake karasawa da kashe su.”

Cikin takardar da aka buga cikin jaridar kimiyya, kungiyar Gladstone ta gano hanyar dake kawo wannan tabon ga kwayoyin garkuwar jikin wanda kuma ya kan kai ga kashe su.

Greene yace “wannan mutuwar CD4 din tafi kusa da kisan kai fiye da kisa daga hannun HIV wani muhimmin abu ne.”
XS
SM
MD
LG