Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dauke Boris Johnson Daga Dakin 'Yan Gobe Da Nisa


Firai Ministan Birtaniya, Boris Johnson

An dauke Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson daga dakin ‘yan-gobe-da-nisa bayan da ya dan murmure daga alamomin cutar Coronavirus da yake fama da su.

Matakin na zuwa ne bayan da Johnson ya kwashe kwana uku a dakin na marasa lafiyan da jikinsu ya tsananta, inda kakakin gidan gwamnati da ke titin Downing ya bayyana cewa yana samun sauki.

Sanarwar na zuwa ne yayin da majalisar dokoki da kafafen yada labaran kasar ta Birtaniya suke kokarin fahimtar zabin da Johnson ya yi na tsohon Minista Dominic Raab.

‘Yan majalisar da kafafen yada labaran, na so ne a fayyace musu yadda za a tafiyar da ragamar mulkin kasar yayin da Firai Minista Johnson ke kwance a asibiti domin jinyyar cutar ta Coronavirus.

Rashin cikakken bayani kan tafiyar da al’amuran gwamnatin na zuwa ne yayin kuma da aka fada wa al’ummar Birtaniya cewa, za su kasance a kulle a gida na karin wasu makonni.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG