Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dauki Matar Da Ta Fi Kowa Kiba A Duniya zuwa Asibiti A Indiya Daga Masar


Jirgin Egypt Air Da Ya Dauki Eman Ahmed
Jirgin Egypt Air Da Ya Dauki Eman Ahmed

An dauki Eman Ahmed 'yar shekara 36, mai nauyin kilo 500 a cikin wani jirgin saman da aka masa wurin zama na musamman daga Masar zuwa Indiya don a yi mata tiyatar rage kiba.

Wata mata yar shekaru 36 yar kasar Misra, wacce ake kyautata zaton itace mace da tafi kowacce mace nauyi a duniya da kilogram 500,an kaita wani asibiti a Indiya domin yimata tiyata domin rage mata nauyinta don ta sami damar yin rayuwa kamar kowa.

A wajen Eman Ahmed, Tafiyar ta zuwa Mumbai itace ta farko fitar ta daga gida a birnin Alexandria cikin shekaru 25. Wanda tafiyar ta hada bukatu da wahalhalu iri iri. Ministan Harkokin wajen India ya shiga maganar wajen nema mata Visa, sannan samar da wuri a jirgin da zai dauke ta da gado na musamman da Babbar Mota wacce zata dauke ta daga filin jirgin sama, inda wani inji zai dauki gadon nata zuwa wuri na musamman da za’a kula da ita.

An haifeta jaririya mai nauyin kilogram 5, Dangin ta sunce ta fara kara nauyi ne tana 'yar shekara 11 ta daina zuwa makaranta a aji biyar a lokacin da ya fara zamar mata wahala ta motsa.

Lamarinta ya kara lalacewa shekaru biyu yayin da ta sami ciwon rabin jiki, wanda ya kai ta ga kasa motsi sannan ya shafi yadda take Magana.

Ba’a san dalilin kibar tata ba , Yan uwanta sun bayyana cewa an tabbatar da tana da ciwo mai suna Dundumi wanda ake kira a turance (elephantiasis), wanda yake sa hannuwa sun kumbura saboda ciwon, Za ayi mata wasu gwaje gwaje a Mumbai domin gane hakikanin abin da yake damunta.

A watan Oktobar bara ne wani likita a Mumbai Mufazzal Lakdawala wanda ya kware a kan abubuwan da suka shafi kiba ya amsa kukan Yar uwarta na neman taimako.

XS
SM
MD
LG