Accessibility links

An daurawa sama da fursunoni 100 aure a garin Cuidad Juarez


Wani gidan yari a Amurka
A kasar Mexico anyi shagulllan daurin aurarraki sunfi 100 – amma a cikin gidajen kurkukun wani gari da yayi kaurin suna da ‘yan hada-hadar miyagun ababan sha masu sa maye.

A garin Ciudad Juarez dake kan iyakar da ta raba Mexico da Amurka ne aka yi wannan hidima inda daya daga cikin angwayen, Andres Dominguez yace watakila auren yasa wasunsu su gyara halayensu in sun gama zamansu na gidan yari.

Jami’in da yayi jagoran addu’oin da aka yi wajen daura aurarrakin, Cesar Fernando Ramirez yace auren wani bangare ne n a shirin gwamnati na taiamkawa fursunonin samun damar mikewa da rayuwa mai kyau idan sun gama zamansu na wakafi. Shi dai wannan garin na Ciudad Juarez gari ne da ya shahara saboda sana’ar miyagun ababan sha da ake a cikinsa da kuma yawan kashe-kashen mutane da akan yi.

A cikin shekaru kadai da suka gabata, kamar mutane 7,000 suka rasa rayukkansu a cikin tashe-tashen hankalin dake da alaka da wannan muguwar sana’ar, kuma da yawan wadanda akan kashen, aka yi jifa da gawawwakinsu ne a cikin hamadar Mexico mai masifar zafin gaske.
XS
SM
MD
LG