Accessibility links

An Daure Dan Tsohon Shugaban Kasar Senegal A Kurkuku


Karim Wade, da Sindiely Wade, 'ya'yan tsohon shugaban Senegal Abdoulaye Wade, a birnin Dakar, Fabrairu 26, 2012.

Ana zargin shi da mallakar dukiya har ta dala biliyan 1 da miliyan 400 ba bisa ka'ida ba.

WASHINGTON, D.C - An jefa Karim Wade a babban gidan yari dake birnin Dakar a yammacin jiya Laraba, bayan da lauyoyin gwamnati suka bada umarnin kama shi, da tuhumarshi da yi wa dukiyar jama'a zagon kasa. Shi da mukarrabansa su bakwai, an daure su ba tare da damar amsar belin su ba.

Lauyoyin gwamnati sun ce, Wade, wanda ya rike mukamai da dama a lokacin da babansa yake mulki, yayi amfani da hanyoyin da ba bisa ka'ida ba wajen mallakar kamfanoni masu matukar tasiri ga tattalin arzikin Senegal.

Wade mai shekaru 44 a duniya, ya musanta wannan zargi, kuma lauyoyinshi sun ce arzikinshi na halal ne.

I yanzu dai, ba'a san lokacin da za'a fara shari'a ba.
XS
SM
MD
LG