Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Da Su Rika Bin Sawun Kasafin Kudin Gwamnatocinsu


Shugaban Najeriya, a lokacin da ya je kaddamar da wani aiki a yankin Calabar a watan Oktobar 2015. (REUTERS/Stringer/Files)
Shugaban Najeriya, a lokacin da ya je kaddamar da wani aiki a yankin Calabar a watan Oktobar 2015. (REUTERS/Stringer/Files)

Rahotanni daga kungiyoyin cikin gida da na waje, sun sha bayyana korafinsu kan yadda ake samun tsaiko da kin aiwatar da kasafin kudade da gwamnatoci ke gabatarwa a matakn daban-daban.

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC tare da hadin gwuiwar hukumar shirin raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, sun nemi ‘yan Najeriya da su rika bibiyar kasafin kudaden da gwamnatoci ke gabatarwa a matakai daba-daban.

Hukumar ta yi wannan kiran ne a wani taron fadakar da jama’a da aka shirya a jihar Bauchi, lura da cewa akan samun gwamnatocin dake gabatar da kasafin kudi ba tare da sun aiwatar da shi ba.

“Manufar taron ita ce ya zamanto an ankarar da mutane cewa al’amarin kasafin kudi, al’amari ne da ya shafe su.” In ji daya daga cikin shugabannin da suka shirya taron.

Har ila yau, taron ya ja hankulan jama'a domin su gane cewa suna da ikon fada a ji a kasafin kudi, inda za su iya tuntubar wakilansu domin su bayyana masu abinda suke so a saka a cikin kasafin kudin.

A lokacin da ta ke bayani, shugabar cibiyar gyara halayyar kangararrun yara, Hajiya Halima Baba Ahmed, ta ce lokaci ya yi da mutane za su rika sanin me ke faruwa da kasafin kudinsu.

“Ya kamata mutane su gane me ke tafiya, an ba da aiki? Kuma ya matsayin aikin? An canja wanda aka bai wa aikin ne ya sa aka samu tsaiko?” In ji ta.

Taron dai ya hada har da shugabannin al’uma da na addinai da kungiyoyin fararen hula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG