Tun kafin wannan kiran tsohon shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya kira kasashen Afirka su samar da takardar kudi ta bai daya, farko a kasashen yammacin Afirka kana da Afirkan baki daya.
Masana tattalin arziki sun kalli maganar daban. Dr. Dauda Muhammad Kontagora wani masanin tattalin arziki yace kasashe kamar na yammacin Afirka na iya taimakawa juna akan shige da fice domin tattalin arzikinsu ya habaka amma yin kudi na bai daya nada nashi matsalolin.
Yace kwazon tattalin arzikin kasashe ba iri daya ba ne. Wata kasa ta fi wata kasa kwazo. Haka ma wata kasa ta fi wata kasa karfin tattalin arziki. Idan aka yi masu kudi na bai daya akwai kasashen da zasu cutu.
Shi ma Alhaji Aliko Dangote ya bayyana bukatar an kawo karshen yin anfani da biza saboda balagiro daga wannan kasa zuwa waccan. Kawai da biza sai bada sukunin yin kasuwanci tsakanin kasashe.
Matakan da wasu kasashe ke dauka na tsaro ko na tattalin arziki su kan shafi makwaftansu. Misali matakin da Najeriya ta dauka na hana shigo da motoci da shinkafa ta kan iyakokin kasa ya yiwa tattalin arzikin Banin da Togo rauni.
A saurari rahoton Babangida Jibrin.
Facebook Forum