Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Aikin Fitar Da Matasa 12 Daga Kogo a Kasar Thailand


Wasu kwararrun 'yan iyo na shirin shiga kogo mai shake ruwa don ceto yaran

Yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ke barazana ga kokarin da ake yi na ceto matasan nan guda 12,

Jami'an a kasar Thailand sun ce an fara aikin ceto yaran nan guda 12 da kocin wasan kwallon kafarsu daga cikin kogon nan da su ka makale ciki.

Wasu kwararrun 'yan iyo 13 daga kasashen waje da kuma wasu na kasar ta Thailand su 5 ne ke wannan aikin. Kowanne daga cikin yaran 12 zai samu rakiyar 'yan iyo biyu. Ana kyautata zaton za su fara fitowa da yaran daga karfe 9 na yamma agogon yankin a yau dinnan Lahadi.

An fara ruwan sama kamar da bakin kwarya a arewacin Thailand inda yaran su ka makale cikin matsattsen kogon mai zurfi wanda ke kuma kunshe da ruwa. Wannan al'amarin na iya tilasta masu ayyukan ceton su kara kaimi ganin yadda kokarin ceto matasan ke tattare da matsaloli.

A halin da ake ciki kuma, iskar shaka ta oxygen da ke cikin kogon ta ragu, wanda hakan ka iya kara galabaitar da matasan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG