Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Aikin Umrah


Dakin Ka'aba a Makka.
Dakin Ka'aba a Makka.

Hukumomin Saudiyya sun bar wasu takaitattun mutane sun gudanar da aikin Umrah a kasa mai tsarki a ranar Lahadi bayan da aka fara sassauta matakan kare yaduwar cutar coronavirus, wadanda aka saka na tsawon watanni.

A watan Maris hukumomin kasar ta Saudiyya suka dakatar da aikin Umrah wanda ke samun halartar miliyoyin mutane daga sassan duniya yayin da annobar COVID-19 ta bazu.

Hakan ya sa kasashen duniya suka saka matakan kulle tare da rufe iyakokinsu don a dakile yaduwar cutar.

A halin da ake ciki, mutum 6,000 kawai ake bari su shiga masallacin, sannan ‘yan kasar ta Saudiyya da mazauna kasar ne kawai ake bari su yi aikin Umrar a wannan mataki na farko da hukumomin suka dauka na bude masallacin.

Baya ga hakan, akan ba kowanne mutum sa’a uku ne kacal ya kammala aikin Umrar.

Alkaluman da cibiyar da ke bin diddigin cutar coronavirus a Jami'ar Johns Hopkins ta fitar sun nuna cewa, mutum 335,997 aka tabbatar sun kamu da cutar sannan 4,850 suka mutu a kasar ta Saudiyya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG