Watan Ramadan shi ne wata na tara a cikin kalandar Musulinci, lokacin da Musulmi su ka yi Imani cewa an saukar da Al-Qur’ani Mai Tsarki zuwa Annabi Muhammad (SAW), wanda mala’ika jibrilu ya kai masa sakon tun a karni na bakwai.
Shi ne kuma watan da ake azumi, addu’o'i da sauran ayyukan ibada, sannan lokaci ne da Musulmi suka fi yin dubi kan ayyukansu na yau da kullum.
Lokaci ne kuma da Musulmi su ke kaucewa daga dukkan nau’in abinci, ko abin sha, ko shan taba da kuma jima’i daga fitowar rana zuwa faduwarta.
Kwanakin goman karshe na watan Ramadan, ana daukar su masu matukar muhimmanci. “Lokacin ne da ake bude kofofin Aljanna guda bakwai. Abu mafi muhimmanci shi ne daren Laylat Al-Qadr, ko “daren da ya fi kowane dare a cikin shekara.
Musulunci ya yi rangwame cewa ba kowa zai iya yin azumin watan Ramadan ba; hakan ya sa aka tsame yara kanana da kuma mata masu juna biyu, ko masu shayarwa daga yin azumin.
Har ila yau, wadanda suka tsufa ko ba su da lafiya za su iya ajiye azumin, amma dole ne su ciyar da mutum daya talaka a kowace rana da ba su yi azumin ba, abin da ake kira Fidya.
Sannan adadin kudin da mutum zai kashe wajen ciyarwar, ya danganta da inda mutum ke zaune.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 24, 2021
An Ceto Ma'aikata 11 Daga Wata Mahakar Zinari a China
-
Janairu 24, 2021
'Yan Sanda Sun Kama Dubban Masu Zanga Zanga A Rasha
-
Janairu 23, 2021
Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Duniya Ya Doshi Miliyan 100
-
Janairu 17, 2021
Wani Ayarin Baki Masu Kaura Na Dosar Amurka Daga Honduras
-
Janairu 16, 2021
India Ta Kaddamar Da Shirin Bada Riga Kafin COVID-19
-
Janairu 11, 2021
WHO Za Ta Aika Wata Tawagar Bincike China
Facebook Forum