Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An fara jigilar 'yan Sudan ta Kudu daga Sudan zuwa gida


Wasu 'yan Sudan ta Kudu sun makale a gabar kogin Kosti

Kungiyar maida ‘yan gudun hijira zuwa kasashensu na ainihi ta fara jigilar ‘yan kasar Sudan ta kudu daga Sudan zuwa sabuwar kasarsu.

Kungiyar maida ‘yan gudun hijira zuwa kasashensu na ainihi ta fara jigilar ‘yan kasar Sudan ta kudu daga Sudan zuwa sabuwar kasarsu. Mafi yawan ‘yan gudun hijira da ake kwasa sune wadanda bace a hanya suka kasa bambanta kan iyakar kasarsu da Sudan.

Jirgin saman fasinja na farko dake daauke da ‘yan gudun hijira 164 ya isa Juba babban birnin Sudan ta kudu yau litinin da rana.

‘Yan gudun hijirar na daga cikin ‘yan Sudan ta kudu dubu goma sha biyar dake jiran barin Sudan su koma gida tun samun ‘yancin kan Sudan ta kudu. Yawan nasu ya haifar da matsalar cunkoso a sansanin ‘yan gudun hijira dake Kosti kudancin Khartoum.

Ministan ayyukan agajin kasar Sudan ta kudu Joseph Lual Acuili, shine ya karbi ‘yan gudun hijrar da saukarsu a filin jirgin sama.

Yyai masu maraba lale da komowa gida, kuma yayi masu alkawarin cewa Gwamnati zata kokarta samar masu matsuguni tunda yanzu basu sanda inda gidejensu na ainihi suke ba.

XS
SM
MD
LG