Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kasuwanci A Wasu Bakin Iyakokin Nigeria Da Cameroon


Mutane na hawan motar haya domin tserewa bayan harin ‘yan Boko Haram, a Bama da wasu sassan arewa maso gabasin Najeriya, 8, ga Satumba 2014.
Mutane na hawan motar haya domin tserewa bayan harin ‘yan Boko Haram, a Bama da wasu sassan arewa maso gabasin Najeriya, 8, ga Satumba 2014.

Yanzu haka an bude wasu bakin iyakokin Nigeria da Jamhuriyar Cameroon, kuma har an fara kasuwanci a wadanan wuraren.

Yanzu haka an bude wasu bakin iyakkon Nigeria da Cameroon da aka kulle da sakamakon rikicin rikicin boko haram.

Yanzu kasuwancin da ake gudanar wa a bakin iyakokin wadannan kasashen ya fara farfadowa,

Haka kuma sojiojin kasashe daban-daban dake aiki wadannan wuraren suna sintiri domin kare matafiya.

Wakilin wannan gidan Radiyon mai aiko da rahotanni daga kasar ta Cameroon Moki Edwan Kindzeka yabi sahun wasu sojojin dake aikin wannan sintiri.

Yace yaga wata bas cike da mutane daga cikin motocin matafiya ta iso garin Amchide dake bakin bakin iyakar Cameroon kuma ta fito garin Maiduguri ne.

Daya daga cikin sojojin dake sintiri kan wannan hanyar mai suna Didier Boumjol ya shaida wa wakilin na VOA cewa wannan bas din ita ce ta ukku data iso wannan gari daga Maiduguri kuma ta kwaso mutane da kaya.

Sojan yace kuma ko wace sai munyi mata binciken kwakwaf.

Yace sai sun bude kuttun ajiye kayan kowace mota domin bincike ko domin ganin ko bata dauko wasu kayayyakin da aka haramta shiga dasu wata kasa zuwa wata kasa ba.

kamar su kwaya da dai duk wani abu da doka yayi hani dashi.

Ita ko Asta Dourumssou wata ‘yar kasar Cameroon ce wadda mijin ta ya rasu sakamakon rikicin na boko haram a wani harin da aka kawo wa garin na Amchide a shekarar 2014, ta shaidawa wakilin na VOA cewa tun daga wannan lokacin ta koma kolofata, garin dake da nisan kilomita 10 da Cameroon.

Tace yau tazo wannan wurin ne domin ta samu labarin cewa tana iya samun kayayyakin data ke bukata na kasuwanci, da ake shigowa dasu daga Maiduguri a Najeriya.

Tace tun lokacin rasuwar maigidanta ita kadai ce ke daukar dawainiyar diyan su guda biyu, kuma kasuwanci take yi, abinda tace tana samun ribar akalla abinda yake kwatankwancin dala 4 kowace rana kuma yana isar su suci su sha.

Babban birnin Maiduguri yana kilomita 130 da garin na Amchide wanda yake cikin kasar Kamaru kuma tun lokacin da rikicin na boko haram yayi Kamari aka rufe wannan bakin iyakar abinda ya kawo katsewar shigar da wasu kayayyakin bukata da ake shiga dasu kasar ta Kamaru ta wannan bakin iyakar.

Amma yanzu Manjo Janar Rogers Nicholas yace an bude wannan bakin iyakar domin ko an durkusad da ayyukan ‘yan taadan boko haram a wannan bakin iyakar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG