Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Shagulgulan Sallah a Najeriya


Mai Martaba Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III
Mai Martaba Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Bayan an tabbatar da ganin sabon wata jiya Alhamis, Sarkin Musulmi ya ayyana yau Juma'a a matsayin ranar Sallah karama.

Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da ganin wata a birane daban-daban cikin kasar da suka hada da Sokoto, Kano, Maiduguri da dai sauransu jiya Alhamis.

A dalilin da haka ne ya ayyana yau Juma’a ranar Sallah karama wadda ta zama daya ga watan Shawwal.

Mai Martaba ya gargadi Musulmi da su zauna lafiya da juna da ma wadanda ba musulmi ba.

Ya kuma yi fatan za’a yi salla lafiya a kuma ci gaba da zama lafiya domin kasar ta ci gaba.

A saurari cikakken sakon Mai Martaba Sarkin Musulmi a wannan faifan da wakilin Umar Faruk Musa ya aiko

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG