Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Shari'ar Radko Mladic A Haque


Tsohon Kwamandan Sabiyawa Radko Mladic a gabankotun kasa kasa a Haque.
Tsohon Kwamandan Sabiyawa Radko Mladic a gabankotun kasa kasa a Haque.

Jiya laraba, Shekaru 20 bayan fara yakin basasar Bosnia Herzegovina, aka fara shari’ar Ratko Mladic a birnin Haque, shine mutuminda ake zargi da aikata laifuffukan yaki mafi muni a lokacin yakin na Bosnia.

Jiya laraba, Shekaru 20 bayan fara yakin basasar Bosnia Herzegovina, aka fara shari’ar Ratko Mladic a birnin Haque, shine mutuminda ake zargi da aikata laifuffukan yaki mafi muni a lokacin yakin na Bosnia.

An bude shari’ar Mladic ne da muwahara daga masu gabatar da kara. Tsohon janar na Sabiyawan Bosnia yana fuskantar tuhume-tuhume guda 11 da suka hada da laifuffukan yaki, kisan kare dangi, da cin zarafin Bil-Adama. Kememe yaki amsa wadannan laifuffuka, a madadinsa sai kotu ta rubuta cewa yaki amsa tuhuma da ake masa.

Mladic, dan shekaru 70 da haihuwa, wanda ya shigo kotu sanye da kot mai ruwan toka, ya nuna alamar ko oho ta hanyar daga babbar yatsa kamar wanda yayi nasara. Ya ci gaba da nuna bijirewa yayinda mai gabatar da kara Dermont Groome yake bayyana irin munanan ayyukan ta’asa na zub da jini, dalla-dalla, da aikata a lokacin yakin, ta wajen amfani da hotuna da kuma vidiyo.

Daya daga cikin laifuffukan da ake zargin Mladic da aikatawa shine harin bam da aka kai kan kasuwar Sarajevo da ya kashe fiyeda mutane 30, ya jikkata wasu 70 a 1995. Mai gabatar kara Groome, ya karanta abinda shaidu suka ce sun gani ya faru.

“Da isa na wurin, dakata, ko kuma ‘yan taku kamin nan, Na lura da cewa akwai mummunan yamutsi. Akwai jini ta ko ina, jini yana gudu kan tituna. Akwai kuma nama daga jikin mutane a warwatse. Da kuma yagaggun tufafin mutane warwatse ta ko ina.”

Masu gabatar da kara suna ikirarin cewa Mladic ya taimaka wajen kitsa mummunan kyamfe na kare-dangi, ta hanyar korar Musulmin Bosniya da ‘yan kabilar kuroshiyawa daga yankunan da shi da masu wannan kyamfe suke son su zamo na ‘yan kabilar Sabiyawa kurum. Daya daga cikin mummunan zargi da ake masa ya danganci kashe mazaje Musulmi dubu takwas, yara da manya, a birnin Srebenica.

Mladic wanda aka kama bara, shine na karshe daga cikin gagga-gaggan da ake zargi suna da hannu a yakin Bosnia. Uban gidan Mladic tsohon madugun siyasar Sabiyawa Radovan karadzic, tuni yana fuskantar shari’a gaban wata kotu ta musamman a birnin na Haque.

Fara shari’ar Mladic jiya laraba, ta ci karo da bayyanar tsohon shugaban kasar Laberiya Charles Taylor gaban wata kotu a birnin na Haque. A cikin jawabi maras kan gado da Charles Taylor yayi wa alkali, yayi zargin cewa shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar an biya su ne kuma aka tursasa su su bada shaidar zur.

Cikin watan jiya ne Alkali ya sami Taylor da laifin tallafawa aka aikata laifuffukan cin zarafin Bil-Adama a Saliyo.

Ana shirin alkalai zasu yankewa Taylor hukunci a wani lokaci nan gaba cikin watan nan. Ana sa ran duka sassan biyu na masu gabatar da kara da masu kare wanda ake zargi zasu daukaka kara.

XS
SM
MD
LG