Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Taron Majalisar Manoman Najeriya, Karo Na 43


Yanzu haka mahalarta taron manoma na Najeriya daga fannoni daban-daban sun dukufa sosai wajan ganin sun gano dabarun da za a bunkasa harkokin noma da kuma tattalin arzikin kasar.

A jiya Talata aka fara taron majalisar manoma ta Najeriya karo na 43 a Umuahiya hedikwatar jihar Abia da ke kudu maso yammacin Najeriya, don inganta noma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Da yake jawabinsa a gurin taron, Dakta Aminu Babandi, wanda ya wakilci Dakta Mohammed Bello Umar, babban Sakataran Ma’aikatar Noma na Tarayya ya ce, dole ne a bunkasa noma tare da tabbatar da cewa mun kirkiro shirye-shiryen da za su samu goyon baya a matakan jihohi da kuma tarayya.

Babandi ya kuma kara da cewa suna duba gurare guda uku inda za su fi mayar da hankali.

Shima Kwamishinan Noma na jihar Abia, Barista Chinedum Elemchi, ya bayyana farin cikinsa lokacin da yake jawabin bude taron, inda ya ce gwamnati tasha kaddamar da shirye-shirye a kokarinta na inganta harkar noma a duk fadin kasar.

Sannan ya kuma ce ya kamata a tattaro sakamakon wadannan shirye-shiryen don dubasu da kyau domin bunkasa tattalin arziki da kuma samar da aikin yi.

Haka kuma taron ya samu halartar mutane daga fannoni daban daban na rayuwa a kokarin da ake na tsara dabarun inganta noma don bunkasa tattalin arzikin kasar.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

Facebook Forum

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG