Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Yanke Hukunci Ma 'Yan Boko Haram Din Kasar Senegal


Shugaba Macky Sall na kasar Senegal

Kasar Senegal ta fara yanke hukunci ma wadanda aka samu da laifukan ta'addanci, ciki har da mambobin kungiyoyin Boko Haram da al-Ka'ida shiyyar Maghrib. Jagoran 'yan Boko Haram shiyyar Senegal ne aka yanke ,masa hukunci mafi tsanani.

A wata babbar shari'a mai nasaba da ta'addanci, wata kotu ta musamman da ke Dakar, babban birnin kasar Senegal, ta yanke hukunci ga wasu da ake zargi da kasancewa 'yan bindiga su fiye da dozin guda, wadanda za su yi fursunan kama daga tsawon shekaru 20 zuwa kasa, saboda tuhumarsu da goyon bayan ta'addanci da kuma samar da kayan aiki ga kungiyoyin 'yan bindiga a fadin kasar.

Ranar Alhamis kotun ta yanke hukuncin kan 'yan bindiga da dama, ciki har da Mukhtar Diokhane da mukarrabansa da aka samu da laifun kasancewa 'yan Boko Haram da kuma al-Ka'ida Shiyyar Maghreb.

Adadin 'yan bindiga 14 aka yanke wa hukunci a yayin da kuma aka wanke mutane 15 daga zarge-zargen da ake masu saboda rashin kwararan hujjoji.

Wadanda aka yanke wa hukuncin na iya daukaka kara.

Mukhtar Diokhane, jagoran tawagar 'yan ta'addan, shi ne ya fi samun hukunci mafi tsanani na kurkukun shekaru 20.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG