Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fatattaki 'Yan Boko Haram a Maiduguri


Sojojin Najeriya A Dajin Sambisa

Sojoji da 'yan kato da gora a garin Maiduguri, sun fatattaki wasu 'yan bidnigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne, wadanda suka doshi babban birnin na Jihar Borno da maraicen yau laraba.

Rahotannin dake fitowa daga garin na cewa tun da misalin karfe 6 na maraice ne aka fara jin kararrakin harbe-harbe da fashe-fashe daga hanyar wani kauye mai suna Kayamla, mai tazarar kilomita 10 daga barikin sojan Giwa.

Mutanen dake zaune ta wannan yankin sun yi ta fita daga cikin gidajensu su na gudu da aka fara jin karar harbe-harbe. Amma kuma mazauna garin sun ce an ga 'yan kato da gora, ko Civilian-JTF su na dosar ta inda 'yan bindigar suke.

Har yanzu ba a ji daga bakin hukumomin sojan Najeriya ba, amma wasu kafofi a garin Maiduguri da kuma shaidu sun ce an fatattaki 'yan bindigar an kuma yi musu mummunar barna.

Irin matakan sojan da ake dauka a kan 'yan Boko Haram a yanzu dai sun nakkasa kungiyar, inda 'ya'yanta ke watsewa. Wannan yunkurin kai harin yana iya zama wani matakin kungiyar na nuna wa duniya cewa har yanzu da sauranta.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG