Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawarwakin Bakin Haure 8 A Wata Motar Tirela A San Antonio, TExas.


Motar tirelar da aka samu gawarwakin bakin haure wajen 8 ciki

A wani al'mari mai ban takaici da tausayi, 'yan sanda sun gano gawarwakin wasu daga cikin dinbin bakin hauren da aka cinkushe su a wata motar tirela.

'Yan sanda a Texas sun ce sun samu gawarwakin mutane 8 da safiyar jiya Lahadi, a bayan wata motar tirela a wurin ajiye motocin katafern kantin nan na Walmart. Mutum na tara ya mutu daga bisani a asibiti.

Wata kamarar tsaro ta nadi hoton wasu motoci na zuwa wurin tirelar da daren ranar Asabar, su na ta jidon mutanen bi-da-bi daga tirelar, sannan sai su rufe ta su sheka da wadanda su ka kwasa.

An gano cewa da dinbin mutane a cikin tirelar ne bayan da wani daga cikinsu ya roki wani ma'aikacin Walmart ruwan sha. Wannan ne ya kai ga shigar 'yan sanda cikin lamarin, wanda ya kai ga gano mutane 30 a raye, ciki har da wasu yara wadanda bisa ga shekarunsu ya kamata a ce su na makarantar firamare, da kuma wadanda su ka mutu, wadanda dukkanninsu maza ne balidai. Hukumomi a asibitocin da aka kai mutanen da ke rayen sun ce 20 daga cikinsu na cikin mawuyatan yanayoyi.

An damke wani mutum dan shekaru 60 da haihuwa a Florida, wanda aka ce shi ne direban motar kuma hukumomi sun ce zai fuskanci tuhunce-thumce a kotu a yau dinnan Litini. Sakataren Tsaron Gida John Kelly ya ce za a yi cikakken bincike.

Ba a yi bayanin kasashen da bakin hauren da ke boye cikin tirelar su ka fito ba. San Antonio dai na daura ne da kan iyakar Amurka da Mexico, to amma akan shigo da bakin haure a sace daga Mexicon da ma sauran kasashen da ke kusa da Amurka ta wajen.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG