Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Michael Flynn Ya Karbi Kudade Daga Kasashen Waje


A man stretches at the Yuyuantan Park in Beijing, China.

Tsohon mai baiwa shugaba Donald Trump shawara ta fannin tsaro, Michael Flynn, ya karbi sama da dala dubu dari biyar daga kasar Turkiyya, ya kuma karbi dubban kudade daga jami’an kasar Rasha duk da cewa an gargade shi a shekarar 2014, a lokacin da ya yi ritaya a matsayin janar din rundunar sojan kasar, akan cewa kada ya karbi kudade daga gwamnatocin kasashen waje.

“Ba mu da hujja, ko kadan, dake nuna cewa ya sami izni daga sakataren rundunar sojan kasar da sakataren harkokin wajen Amurka akan ya karbi kudaden daga gwamnatocin kamar yadda doka ta tanada”, kamar yadda dan majalisar wakilai na jam’iyyar Democrat da ke kwamitin binciken, Elijah Cummings, ya bayyana a jiya Alhamis a lokacin da ya gabatar da takardun da aka samo game da binciken Flynn.

Daya daga cikin takardun sun nuna cewa ofishin Speto-Janar din ma’aikatar tsaron Amurka, ya fara gudanar da nasa binciken akan ko Flynn ya nemi iznin karbar kudaden daga gwamnatocin kasashen waje ko a’a, abin da kuma ke cikin binciken da ‘yan majalissar ke yi.

Mai magana da yauwan fadar shugaban Amurka ta White House, Sean Spicer, ya ce ma’aikatar tsaron Amurka za ta tabbatar da cewa idan abin da Flynn yayi ya sabawa doka.

Amma kuma Sean Spicer ya ce gwamnatin Trump ba ta binciki Flynn ba kafin a bashi aikin mai baiwa shugaban ‘kasa shawara a fannin tsaro ba, saboda ta dogara ne kan sabunta binciken da aka yi na shekarar 2016, lokacin gwamnatin da ta gabata, wanda kuma shi Flynn ‘din ya yi tafiya zuwa Rasha ne a shekara ta 2015.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG