Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi Shugaba Joseph Kabila ya Cika Alkawari ya Sauka Mulki


Aminbanu Memon wearing an oxygen mask sits in an auto-rickshaw waiting to enter a COVID-19 hospital for treatment in Ahmedabad, India.
Aminbanu Memon wearing an oxygen mask sits in an auto-rickshaw waiting to enter a COVID-19 hospital for treatment in Ahmedabad, India.

Majalisar Dinkin Duniya tayi kira ga shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyar Congo Joseph Kabila da ya cika alkawarinsa na sauka daga karagar mulki, yayin da kasar ke fama yawan zanga zanga a kan jinkirin gudanar zabe.

Babban sakataren MDD yayi kira ga manyan yan siyasar Congo da su bada cikakken hadin kai ga yarjejeniyar da suka kulla ta 31 ga wata Disemban 2016 wanda ya bukaci Kabila ya sauka daga mulki bayan zabe.

Amma kuma ana ta jinkirta zabukan da akayi alkawarin gudanarwa a shekarar 2017 da ta kare, lamarin dake ci gaba da haddasa tashe tashen hankula da kuma haifar da fargabar Kabila na niyar yin tazarce.

Shi dai Kabila mai shekaru arba'in da shida a duniya ya kwashe shekaru goma sha bakwai yana shugabancin kasar Congo-Kinshasha kuma har yanzu yana nan daram akan karagar mulki, duk da cewar wa’adinsa na biyu ya kare tun a cikin watan Disemban shekarar 2016.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG