An kammala zaman tattauna yadda za a shawo kan rikicin siyasar kasar Libya, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani, ba tare da an cimma wata kwakkwarar matsaya ba.
Sai dai an amince cewa za a sake haduwa a watan Maris mai kamawa.
Taron dai ya faro ne da tangarda, tun ma kafin a fara tattaunawa, inda mambobin bangarorin da ke takaddama da juna suka janye daga zaman.
Hakan ya sa wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman da ke jagorantar sulhun, Ghassane Salame, ya nuna rashin jin dadinsa tare da cewa an shammace shi.
“Mun yi mamaki, ranar da ya kamata a ce an fara taron, sai ga shi an ce wasu su fita a dakin taron.” in ji Salame.
Ita dai Libya ta shiga rudanin siyasa na baya-bayan nan ne, tun lokacin da ‘yan tawayen sojoji masu goyon bayan Khalifa Haftar suka kai hari kan birnin Tripoli, inda nan ne fadar gwamantin da kasashen duniya suka amince da ita.
Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,000 ya kuma raba wasu dubbai da muhallansu.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
NIJAR: Bazoum Mohamed Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
-
Fabrairu 23, 2021
Wai Ko Wa Ake Ganin Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa A Nijar?
-
Fabrairu 22, 2021
Ana Jimamin Mutuwar Jami'an Zabe Bakwai Da Suka Rasu a Nijar
-
Fabrairu 21, 2021
ZABEN NIJAR: Nakiya Ta Hallaka Jami'an Zabe 7 a Yankin Tillaberi
-
Fabrairu 21, 2021
Ana Ci Gaba Da Kada Kuri'ar Zaben Sabon Shugaban Kasa A Jamhuriyar Nijar
-
Fabrairu 20, 2021
ZABEN NIJAR: Yadda Aka Kammala Yaki Neman Zabe, CENI Mun Shirya Tsaf