Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Taimakawa Bangaren Lafiya A Najeriya


Taro Don Taimakawa Bangaren Lafiya A Najeriya
Taro Don Taimakawa Bangaren Lafiya A Najeriya

Kamfanin tsare-tsare da bincika na Duke tare da hadin gwiwar Gidauniyar tattalin arziki na Musulunci a Africa sun gudanar da taron na musamman don tattauna hanyar  za’a kawo sabbin dabarun duba marasa lafiya a matakin farko tare da basu magani cikin sauki ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Taron wanda aka gudanar a Abuja, ya samu halartar manyan baki da sauran masu ruwa da tsaki musamman a bangaren lafiya a fadin Najeriya da suka hada da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau, Sanata Umar Abubakar Gada, Umma K Ahmed daga ma’aikatar lafiya ta Kaduna, Alhoussaine Bah daga Bankin Cigaban Musulunci da sauran su.

Taken taron shine hanyar hada-hadar kudi na Musulunci: Duba sabbin hanyoyin samar da kudi don kawo sauyi a bangaren lafiya matakin farko a Najeriya.

Taro Don Taimakawa Bangaren Lafiya A Najeriya
Taro Don Taimakawa Bangaren Lafiya A Najeriya

Shugaban kanfanin tsare-tsare da bincika na Duke, Dr. Kabir Umar Dasuki yace manufar tasu ta samu asali ne daga kasashen India da Birtaniya, kuma sun yi amfani da wannan na’aura a lokacin annobar cutar korona, yace kawo wannan na’ura zai taimaka wajen inganta lafiyar mutane musamman a kauyuka.

Shima shugaban Gidauniyar tattalin arziki da sarrafa kudi na Afurka, Baba Yunus Muhammad yace gwamnatoci na bukatar tallafi don bukasa harkar lafiya don haka zasu taimaka don ganin an cimma manufa.

A nasa bangaren Farfesa Ahmad Bello Dogarawa na Jami’ar Ahmadu Bello dake zaria yace wannan shine karon farko da aka yi taron don tallafawa harkar lafiya dake da alaka da hanyar sarrafa kudi na Musulunci saboda haka abun maraba ne.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG