Wata kungiya mai zaman kanta mai fafutikar hada kawunan al'umma tare da wanzar da zaman lafiya ta shirya taron da ya samu halartar wakilan kungiyoyin 'yan Biafra da arewacin Najeriya da na Miyetti Allah da kungiyar Oduduwa ta Yarbawa.
Manufar taron ita ce tabbatar da wanzar da zaman lafiya a duk fadin kasar Najeriya, walau tsakanin kungiyoyi ko kabilu.
Alhaji Salisu Ba Son Kai sarkin Fulanin Shagamu yace sun shawo kan matsalar makiyaya da manoma kuma ashirye suke su taimaka wajen kawo zaman lafiya tsakaninsu da manoma ko kuma wasu a duk lokacin da aka bukacesu su yi hakan. Sun shiga lungu lungu suna wayar da kawunan mutane.
Sai dai wasu na ganin ba yin taro kodayaushe ba ne zai tabbatar da zaman lafiya a Najeriya muddin babu adalci tsakanin shugabannin al'umma ko na gwamnati da talakawan da suke yiwa jagora, inji Malam Musa Jika.
Yana mai cewa "wannan mu a wurinmu ba shi ne mafita ba kuma ba shi ne matsala ba. Abun da yakamata gwamnati ta yiwa mutane abun da ya dace...Duk tashe tashen hankali ba wani abu yake haddasu ba illa rashi da ya yiwa mutane katutu".
Mutane basu da kudi, basu da lafiya kana babu cikakken tsaron al'umma da za'a kula da lafiyarsu da kuma dukiyoyinsu. Ya cigaba da cewa zaman lafiya ba zai yiwu ba idan mutum na fama da yunwa. Bugu da kari akwai rashin adalcin shugabanni dake cikin wadata yayinda talakawa ke cikin mummunan matsi. Kamata yayi gwamnati ta yi wani abun da zai taimaki rayuwar al'ummarta.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum