Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Wani Zanga Zanga A Birnin Moscow


Dubban ‘yan kasar Rasha ne suka hau kan tituna a fadin kasar a yau lahadi don zanga zanga akan Cin hanci da Rashawa da kuma bukatar Firaminista Dmitry Medvedev ya sauka daga kan mukamin sa, a gangamin da shugaban adawa Alexei Navalny ya kira.

Zanga zangar ta zamo mafi girma da aka taba shiryawa wacce ta nuna rashin jin dadi tun bayan zanga zangar da akayi a tsakanin shekarar 2011 da 2012 wacce ta biyo bayan Almundahana da ta sahfi zaben ‘yan majalisu.

Har yazuwa tsakiyar rana a Moscow, gidajen Talabijin na Jiha basu bada rahoton zanga zangar ba, Amma shafukan labarai na yanar gizo da kuma na sada zumunta sun rawaito labarin zangazangar a biranen Vladivostok a can gabashin Yekaterinburg a UralsAn bada rahoto kame wasu da yawa daga cikin masu zanga zangar.

Navalny ya kira zanga zangar ne bayan buga wani cikakken rahoto a farkon watan nan wanda yake zargin Medvedev da Mallakar Manya manyan gidajen Alfarma da jiragen ruwa na alfarma gami da Gidajen gona a karkashin wata boyayyiyar kungiya wacce hankalinta bai karkata wajen neman ribaba.

An kalli rahoton a shafin yanar gizo na youtube fiye sai miliyan guda. Har izuwa yanzu Medvedev bai ce komai bad an gane da zargin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG