Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zaben Kanannan Hukumomi A Mali


Wata mata na kada kuri'arta a kasar Mali

Kasar Mali ta gudanar da zaben kananan hukumomi da aka dade ana jinkirtawa.

An soke zaben a wasu mazabu da yawa sakamakon matsalar rashin tsaro da ya addabe su, tare da sace wani dan takara da akayi.

Mayakan Jihadi sun mamaye wasu garuruwan wanda hakan ya taimaka wajen jinkirta zaben.

Shugaban Kasa Ibrahim Bubakar y ace a yayin da yake kada kuri’arsa, “ An daga wannan zabe har sau hudu, Ya isa haka”.

Sakataren MDD Ban Ki-Moon yayi kira da ayi zabe cikin kwanciyar hankali “ wanda siyasa da tsaro zai bada damar yinsa”.

Mali ta fuskanci barazanar tabbatar da zaman lafiya sakamakon Yaki da masu fafutukar Jihadi a Arewacin kasar.

XS
SM
MD
LG