Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba'amariken da Ya Taimakawa ISIS Zai Yi Zaman Kaso Na Shekaru 30


Mayakan sa kai na ISIS

An yankewa wani baAmurke dan asalin kasar Somalia hukunci daurin zaman gidan yari na tsawon shekaru 30 bisa laifin taimakawa kungiyar IS da kayan aiki.

Mohamed Farah mai shekaru 22 da haifuwa yana cikin matasan Somalia guda tara dake jihar Minnesota da aka yanke musu hukunci dauri a wannan mako bisa laifin saboda anniyarsu ta shiga kungiyar IS da kuma shirya kisan kai a wata kasa ta waje.

Farah yana cikin mutane uku da suka ki yarda da laifinsu inda aka mika shari’arsu ga komitin masu yanke hukunci na kotu don su zartad da hukunci a kansu.

An sameshi da laifin inda a cikin watan Mayu ya yi kokarin shiga kungiyar IS don yi kisa a kasashen waje.

A ranakun Litini da Talata ne aka yankewa wasu mutane biyar hukunci ciki har da dan uwan Farah din, watau Adnan Farah mai shekaru 22 da ya amince da laifinsa, kuma shima an yanke masa hukunci dauri na shekaru 10 a gidan yari.

Masu shigar da kara sun ce wa’yannan matsa suna cikin wani gungun abokai dake ba juna kwarin guiwan shiga cikin mayaka kungiyar IS a shekarar 2014. Wasu abokan nasu sun isa kasar Syria amma su taran basu tafi ba.

Saura mutane biyu da suka rage Abdirahaman Dauda da Guled Moar a ranar Laraba mai zuwa ce za a yanke musu nasu hukunci.

XS
SM
MD
LG