Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Kasahen Yammacin Turai Saboda Mata


Women Protesting Against Rape in Kano
Women Protesting Against Rape in Kano

An gudanar da zanga-zangar lumana a kaashen yammacin Turai domin karrama ranar kare mata a duniya,inda da farko an samu tirjiya a kasar Turkiyya kafimn muhunta su sa baki.

Dubban jamaa ne suka gudanar da zanga-zangar lumana a kasashen yammacin turai domin karrama ranar bikin yaki da cin zarafin mata a duk fadin duniya.

Musali a Paris, daruruwan mutane suka yi maci bayan da shugaban kasar Emanuel Macron ya bayyana cewa zai samar da wasu hanyoyin da za a dakile hanyar takura wa mata a cikin kasar.

Yace mata 123 ne wata tsohuwar kawar Faransa ta hallaka a shekarar data gabata.

Yace daya daga cikin matakan ko da za a dauka domin magance aukuwar hakan shine samar da doka mai karfin gaske wanda zata hukunta duk wani da aka samu da lafin cin zarafin mata, kana za a kara wa mata kwarin gwiwa da game da ilmin yin hakan.

Yace yana fata ganin wadanda wannan balain na cin zarafi ya rutsa dasu su zamanto sun fita daga irin wannan damuwar.

A Rome ma anyi irin wannan jerin gwanon ciki ko har da masu gidajen dake baiwa mata mafaka musammam wadanda suka tsere domin gudun tursasawar mazajen su ko kuma samarin su.

Masu Zanga-zangar sun bukaci ‘yan siyasar Italiya da su mayar da hankali akan samar da kudi da za ayi anfani dasu domun taimakawa cibiyoyi dake da alaka da mata.

Amma a kasar Turkiyya da farko ‘yan sanda sunyi yunkurin hana su, sun ace musu wannan zanga-zangar nasu ya sabawa doka amma daga bisani yan sandan suka tattauna da jamiian majilisar dokokin kasar wadanda suka bada umurni a kyale su.

An dai gudanar da ire-iren wadannan zanga-zangar a kasashe kamar su Brazil, Mozambique, Turkiyya da dai sauran su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG