Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Zangon Farko Na Wutar Lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana A Morrocco


Aerial view of the Noor 1 solar plant in central Morocco, Feb.4, 2016.

Sarki Muhammadu na 6 na Morrocco ya kaddamar da zangon farko na hasken wutan lantarki mai anfani da hasken rana wanda wannan shine mai girman gaske irin sa na farko a duniya.

Samar da wannan dai zai rage ko kawar da gurbatar yanayi.

Shi dai wannan katafaren abin samar da hasken wutan lantarkin an kafa shi a wajen birnin Quarzazzate, daura da hamada.

Da yake jawabi wajen kaddamar da wannan katafaren abin samar da hasken wutan lantarkin Ministan Muhalli na kasar Faransa Segolelence Royal yace wannan ya nuna cewa ana iya samar da wadataccen hasken wutan lantarki ta hanyar anfani da hasken rana, yace wannan sako ne ga shugabannin Africa dama duniya baki daya.

Shi dai wannan an tsara shi ta yadda zai iya adana hasken rana da za a sarrafa shi zuwa haske idan dare yayi ko kuma lokacin duhun hadari.

Girman sa ko yakai girman madubayya maka-maka har dubu dari biuya wadanda dasu ne zaa rika adana hasken kuma an baza su ne a filin da yakai girman filin kwallo akalla 600.

Wani kanfanin kasar Saudiyya ce ta gina shi da agajin kudi da kasar ta tattara daga hukumomin kasar daban-daban, cioki ko har da bankin duniya da kuma bankin raya Africa

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG