Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gwabza Fada Tsakanin 'Yan Tawayen Abzinawa Da 'Yan Kishin Islama A Mali.


Al Kahedi Cissé, wani babban jami'in 'yan gwagwarmaya a arewacin Mali.

Shaidun gani da ido sun bada labarin gwabza fada a tsakanin ‘yan tawayen Abzinawa da mayakan kungiyar kishin Islama a Arewacin kasar Mali.

Shaidun gani da ido sun bada labarin gwabza fada a tsakanin ‘yan tawayen Abzinawa da mayakan kungiyar kishin Islama a Arewacin kasar Mali.

Mazauna birnin Gao sun bayyana cewar da hantsin yau laraba aka rika tafka fada a tsakanin mayakan Buzaye na kungiyar ‘yan tawayen MNLA da kungiyar Kishin Islama ta MUJAO. Wakilin muryar Amurka yace mazauna birnin sai guduwa suke yi zuwa gidajensu domin samun mafaka.

Hadin gwiwar kungiyoyin biyu, ta‘yan tawayen Abzinawa MNLA da kungiyar Ansar Dine masu kishin Islama ne suka mamaye Arewacin mali suke kuma gudanar da mulkinsa tun farkon shekarar nan ta Miladiyya. Babu wani rahoton samun jikkata amma cikin makonnin baya aka faro wnanan takun sakar a tsakanin kungiyoyin biyu.

A can Bamako, babban birnin kasar Mali kuma, ‘yan Arewacin malio dake gudun hijira sun gudanar da zanga-zanga a kwanaki biyu a jere domin yin kira ga Gwamnatin Mali da ta tura soja suje su sake kwato yankin nasu daga hanun ‘yan tawayen dake ayyana ballewa.

XS
SM
MD
LG