Accessibility links

An kashe wadansu Turawa biyu da ake yin garkuwa da su a Najeriya a lokacin da sojojin Najeriya da na Britaniya suka yi kokarin kwato su

An kashe wasu Turawa biyu da ake yin garkuwa da su a Najeriya a lokacin da sojojin Najeriya da na Britaniya suka yi kokarin kwato su.

Gwamnatocin Britaniya da Italiya sun fada yau alhamis cewa da alamun mutanen da suka sace wadannan turawa biyu ne suka kashe su.

A watan Mayun bara aka sace wadannan turawa biyu, Franco Lamolinara dan kasar Italiya da Christopher McManus dan kasar Britaniya a arewacin Najeriya.

Gwamnatin Italiya ta ce hukumomi sun kaddamar da farmakin neman ceto mutanen a saboda ana fargabar cewa ana dab da hallaka su.

Sanarwar ta Italiya ta ce sojojin Najeriya tare da tallafin Britaniya ne suka kai farmakin neman kwato mutanen.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG