Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An hallaka wasu 'yan sandan Misira guda 13 a wani hari


Shugaban Kasar Misira, Abdel-Fattah el-Sissi
Shugaban Kasar Misira, Abdel-Fattah el-Sissi

Hukumomi a Misira sun ce akalla an kashe ‘yan sanda 13 a jiya Asabar a wani harin da aka kai shingen binciken jami’an tsaro a babban birnin El-Arish da ke Yankin Zirin Sanai.

Ministan cikin gidan Masar ne ya tabbatar da faruwar lamarin. Mayakan kungiyar ta’addar ISIS sun dauki alhakin kai wannan hari, inda suka ce sun aika da dan kunar bakin wake ne da ya tada kansa da motar da ya makaro da ababen fashewa.

Zirin Sanai dai yana fama da ‘yan ayyukan ta’addanci sannu-sannu na tsawon shekaru da dama tun bayan barkewar boren ‘yan Misira wanda har Sojoji suka hambarar da gwamnatin Shugaba Mohammed Morsi a shekarar 2013

In ba a manta ba a watan Oktobar shekarar 2015 da ta gabata sai da ‘yan ta’adda suka harbor wani jirging saman fasinja na kasar Rasha, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 224 suka mutu.

XS
SM
MD
LG