Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Haramta Zanga-Zanga A Kasar Guinea-Conakry


Shugaban Burkina Faso, Blaise Compaore (tsakiya) wanda ke kokarinw arware rikicin siyasar Guinea, tare da 'yan takarar biyu, Cellou Daleine Diallo (dama) da Alpha Conde (hagu) ran 3 ga watan Satumba, 2010 a fadar shugaban Burkina, a Ougadougou

Haramtawar ta biyo bayan kashe mutum guda da raunata wasu masu yawa a bai wa hammata iska a tsakanin magoya bayan 'yan takara a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da za a yi ranar lahadi mai zuwa

Hukumomi a kasar Guinea-Conakry sun haramta yin zanga-zanga a titunan kasar a bayan da aka kashe mutum guda, aka raunata wasu akalla hamsin a fadan da aka gwabza tsakanin magoya bayan ‘yan takara masu hamayya da juna a zaben fitar da gwani na shugaban kasa da za a yi.

Magoya bayan ‘yan takarar biyu, Cellou Dalein Diallo da Alpha Conde, sun ba hammata iska a titunan birnin Conakry a ranakun asabar da lahadi. Sai da ‘yan sanda da dakaru suka shiga tsakani domin kawo karshen fada a tsakanin sassa masu jifa da duwatsu da kai farmaki kan motoci.

Kowannensu yana zargin daya bangaren da laifin tayar da wannan fada.

Tankiyar siyasa ta kara zafi a kasar Guinea tun ranar alhamis, a lokacin da aka yanke hukumcin daurin shekara guda-guda a kan wasu manyan jami’an zabe na kasar a saboda zarginsu da laifin aikata magudi a zagayen farko na zaben shugaban kasa a watan Yuni.

Diallo, wanda ya taba rike mukamin firayim minista, shi ya zo na daya a zagayen farko da kashi 44 cikin 100 na kuri’un. Conde, wanda ya jima yana dan hamayya, ya zo na biyu da kashi 18 cikin 100. Mutanen biyu zasu kara da juna a zaben fitar da gwani ranar lahadi mai zuwa.

XS
SM
MD
LG