Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Zaben Fitar Da Gwani Na Shugaban Kasa A Guinea


Marigayi shugaban hukumar zaben Guinea Conakry, Ben Sekou Sylla, yana magana da shugabar majalisar mika mulki ta kasar, Rabiatou Sera Diallo lokacin wani taron shugabannin jam'iyyun siyasa a Conakry.

Jami'an zabe sun ce sun dage wannan zabe na ranar lahadi, amma ba su tsayar da sabuwar ranar da za a gudanar da shi ba

Jami’an zabe a Guinea-Conakry sun ce sun dage zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa ranar lahadi a kasar. Wannan zabe ya fada cikin halin rashin tabbas a sanadin zarge-zargen shirya magudi, da mutuwar shugaban hukumar zabe da kuma fadace-fadacen siyasa.

Jami’an zabe sun fada cikin daren laraba cewa har yanzu ba su tsaida sabuwar ranar yin zaben ba. Suka ce daya daga cikin dalilan jinkirta wannan zabe shi ne rashin kayan zabe, har suka ce za a dauki tsawon makonni biyu kafin a warware.

An shirya zaben ne a tsakanin tsohon firayim minista Cellou Dalein Diallo da dadadden shugaban hamayya Alpha Conde.

A ranar lahadi hukumomin Guinea suka dakatar da yakin neman zabe a bayan da aka kwashe kwanaki biyu ana ba hammata iska a tsakanin magoya bayan ‘yan takarar.

A ranar litinin, shugaban hukumar zabe ta kasar Guinea ya mutu a wani asbitin birnin Paris a kasar Faransa a sanadin wata cutar da ba a bayyana ba. Kwanaki kadan kafin a garzaya da shi zuwa asibitin kuwa, kotu ta same shi da laifin yin magudi ta hanyar sauya sakamakon zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka yi a watan Yuni har ta yanke masa hukumcin daurin shekara daya a kurkuku.

XS
SM
MD
LG