Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harba Manyan Bindigogi A Mogadishu Kusa da Wajen Zaman Majalisar Kasar


Sojojin Somalia sun yi shirin ko ta kwana saboda zaben shugaban kasa da za'a yi yau Laraba

A Somalia, al-barusan manyan bindigogi biyar ne suka tashi kusa da tashar jirgin saman kasar dake Mogadishu a daren jiya Talata, gabannin zaman majalisar dokokin kasar a yau Laraba, indazasu zabi sabon shugaban kasar. Fashewar ta auku ne kilomita daya daga inda za'a gudanar zaben.

Nan da nan dai babu rahotanni kan wadanda suka jikkata daga hare haren. Wasu mazauna yankin suna zargin kungiyar mayakan sa kai ta al-shabab, wacce ta sha alwashin zata kassara zaben.

Haka nan a waje birnin na Mogadishu ma,mutane da ake zargin mayakan sa kai ne sun kaddamar da hari da manyan bindigogi kan sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar hada kan Afirka ko AU a daren jiya Talatan, kamar yadda wani jami'in kasar yayi bayani wanda bashi da nisa d a sansanin, sai'ilnda aka kai harin Arabow mai tazarar kilomita 13 daga birnin na Mogadishu.

Shugaban kasar mai ciyanzu yana neman wani sabon wa'adi inda zai kara da wasu 'yan takara ciki harda mutuminda ya karbi iko daga hannusa da wasu tsoffin Firayim Ministocin kasar biyu.

XS
SM
MD
LG