A yau Talata ne wani mutum ya harbe kansa da wasu mutane 6 a wani asibiti a gabashin birnin Ostrava na kasar Czech, alamarin da wasu ke bayyanawa da babban tashin hankali a kasar.
Maharbin, dan shekaru 42, ya fara harbi tun daga isarsa wurin da ake kula da masu bukatar kulawar gaggawa na asibitin Ostavia wanda ke kilomita 300 a gabashin kasar Prague. Kuma A cikin 'yan mintoci kadan ya halaka maza 4, da mata 2, al’amarin da 'yan sanda suka ce ba su da masaniya kan dalilin wannan mutum na daukar wannan mataki.
Maharbin nan take dai ya yi kokarin tserewa daga hukuma, amma ko da ya ga sun rutsa shi, sai ya daga bindigar ya harbe kansa.
Manajan wurin da maharbin ke aik, ya shaida ma 'yansanda cewa maharbin na da tsananin ciwon da ba mai kula da shi ko a asibin, wanda shi ne dalilin da ya haifar da wannan tashin hankali.
Firaministan kasar ya soke tafiyarsa zuwa kasar Estonia, kuma shugaban kasar Milos Zeman ya nuna matukar damuwasa da jajantawa al'ummar kasar da na iyalen wadanda alamarin ya shafa.
Facebook Forum