Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Wata Mawakiya Har Lahira a Amurka


Mawakiya Christina Grimmie, a lokacin tana raye

A nan Amurka, an harbe wata mawakiya har lahira, wacce ta lashe gasar waka da gidan talbijin na NBC ke shiryawa.

Christina Grimmie na rattaba hanunta akan kayayyakin da masoyanta suka mika mata a jiya Juma’a a birnin Orlondo da ke jihar Florida, sai wani dan bindiga ya bude mata wuta.

Dan uwan mawakiyar, wanda ke kusa da ita, ya yi yunkurin cafkar dan bindigar domin kare ‘yar uwarsa, amma sai ya makara.

‘Yan sanda sun ce dan bindigar ya harbe kansa har lahira bayan da ya kashe Grimmie.

A shekarar 2014, Grimmie mai shekaru 22 ta zo ta uku a gasar wakar.

XS
SM
MD
LG