Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi Mutane 15 A Wani Gidan Rawa A Amurka


Jami’ai a Cincinnati dake tsakiyar Yammacin Amurka a Jihar Ohio, sun ce a kalla mutane 15 aka harba daya daga cikin su mummunan harbi a wani gidan rawa da yake a makare da mutane a safiyar lahadi.

Jami’in Yan sanda (Mataimakin Shugaban Yan sanda Neudigate) yace yanayi a Cameo Night Club “Mummunan yanayi ne.”

Yace daruruwan mutane na cikin club din yayin da maharbin ya bude wuta.

Gidan talabijin na WLWT ya bada rahoton da yawa daga cikin wadanda harbin ya shafa na cikin mummunan yanayin da zasu iya rasa rayukansu, kuma jami’a basu yi bayanin ko an kama wani domin tuhuma ba.

Jami’ai sun ce mai yiwuwa maharban na da yawa. Izuwa yanzu dai babu hakikanin masaniyar abinda ya jawo mummunan al’amarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG