Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi Wani Dan Majalisar Amurka A Kwankwaso


Daya Daga Cikin 'Yan Majalisar Da Aka budewa Wuta Rep. Mo Brooks.
Daya Daga Cikin 'Yan Majalisar Da Aka budewa Wuta Rep. Mo Brooks.

Wani dan bindiga dadi ya budewa 'Yan Majalisa na Jami'iiyar Republican wuta yayin da suke wasan kwallon kulki.

An harbi wani dan majalisar wakilan tarayya ta Amurka mai suna Stephen Scalise yau laraba a garin Alexandria dake kudu a bayan garin nan birnin Washington, a yayin da shi da wasu ‘yan majalisar ‘yan jam’iyyar Republican suke wasan kwallon kulki.

An ce Scalise yana samun jinya a wani asibiti a nan Washington a bayan da aka harbe shi a kwankwaso.

Rahotanni sun ce da alamun mutane biyar ne suka ji rauni a lokacin da wani dan bindiga ya bude musu wuta a lokacin wannan wasan kwallon kulki da sanyin safiyar nan. ‘Yan sandan birnin Alexandria sun fada a shafinsu na Twitter cewa sun tsare wanda ake kyautata zaton ya kai harin.

Shugaba Donald Trump yace shi da mataimakinsa Mike Pence suna sanya idanu kan lamarin. “Muna bakin cikin wannan abin alhini, in ji shugaba Trump cikin wata sanarwa.

Scalise shine mai tsawatarwa na masu rinjaye a majalisar wakilai, mukamin da ya ba shi ikon tabbatar da yin biyayya ga manufofin jam’iyyar Republican a tsakanin wakilanta a cikin majalisa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG